CORONAVIRUS: Gwamnati za ta maida filayen wasanni da sansanonin NYSC wuraren killace mutane

0

Gwamnatin Najeriya da umarci ma’aikatar wasanni da ta bude filayen wasanni dake Kaduna, Legas, Abuja da Ibadan domin yin amfani da su wuraren kula da killace mutanen da suka kamu da cutar coronavirus.

Gwamnati ta ce ba nan ba kawai za a yi amfani da wuraren da ake horas da dalibai masu Yi was kasa hidima a fadin kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar 18 ga watan Maris hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta dakatar da horas da su saboda diran coronavirus a Najeriya.

Hukumar ta kuma rarraba wa daliban wasikun tura su wuraren da za su yi aikin yi wa kasa hidimma Kai tsaye a wancan lokaci

Ministan wasanni Sunday Dare ya sanar cewa gwamnati ta yi haka me domin samar da isassun wurare da za a kula da mutane ko da cutar ta barke a kasar.

Dare yi kira ga mutane da su guji yada labaran karya kan cutar cewa idan dai aka hada kai za a samu nasaran kawar da cutar.

Bayan haka a ranar Alhamis Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta mai da cibiyar kula da masu fama da cutar daji (ICCA) asibitin kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan.

A yanzu dai mutane 65 suka kamu da cutar a Najeriya.

Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS

1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.

2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.

3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.

4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.

5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.

6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa

7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.

8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.

9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.

10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.

Share.

game da Author