Ministan Yada Labarai ,Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnati na farautar mutane sama da 4000 da yakamata su zo ayi musu gwajin cutar.
Lai ya ce ‘Yan Najeriya na basu wahala matuka a wannan aiki da suka sa a gaba, Yana mai cewa wasu da gangar suka rubuta adireshin karya a takardun su bayan sun diran Najeriya daga kasashen waje.
” Yanzu Muna farautar su ruwa a jallo domin ayi musu gwajin jini, Amma abin ya faskara. Ba a iya gano su ba saboda adireshin karya da suka saka a takardun su na tafiya.
” Muna duk Wanda ya dawo kasar nan daga waje su gaggauta garzayowa a yi musu gwaji. Idan mutum ya kamu da cutar coronavirus bai zama dole shi kenan zai mutu ba. In ba haka ba kuwa suna sa duka mutanen kasa cikin hadari ne babba.
” Sannan kuma dokokin da aka saka mutane basu bi. Har yanzu zaka ga mutane na taro da sauran su.
Yanzu a dalilin haka, gwamnati na so ta saka tsauraran dokoki domin tilasta wa mutanen Najeriya su bi umarnin ta.
Cikin wadannan Dokoki harda rufe tashoshin motoci, da shiga da ficen jihohi da garuruwa.
A karshe Lai Mohammed yayi Kira ga wadanda suka San ya kamata ayi musu gwaji si garzayo ayi musu gwajin tun da wuri.