CORONAVIRUS: Bambanci tsakanin Bullar Cuta, Yaduwar Cuta da kuma Barkewar Annoba

0

Wannan wani sahihin bayani ne PREMIUM TIMES HAUSA ta fassara a takaice. Farfesar Ilmin Sanin Barkewar Annoba, Rebecca SB Fischer ta Jami’ar Texas, Amurka ce ta yi bayanin, aka fassara domin amfanin masu karatun mu.

Bullar Cuta: Aka ce cuta ta bulla, to ana nufin farkon bayyanar ta a jikin wani ko wasu a wani gida, shiyya, unguwa ko gari guda daya. A wannan lokaci wani ne ki wasu kadai kan kamu, wadanda suka yi kusanci da wanda ya kamu din.

Sannan kuma idan aka dauki matakan gaggawa na killace su, hana su shiga jama’a da kuma hana jama’a cakuduwa da su, to za a dakile cutar a hana ta bazuwa cikin jama’a.

Idan kuwa ta bazu a cikin garin, to hana shiga da kuma gagauta daukar matakan gaggawa ne maganin hana barkewar ta.

Yaduwa Ko Bazuwar Cuta: Ana nufin idan annoba ta fita daga wata unguwa ta mamaye gari, har ta kai cutar ta bazu cikin wasu garuruwa, to shi ake kira Yaduwar Cuta ko Bazuwar Cuta, a Turance ta zama ‘epidemic’ kenan.

Shawo kan annobar da ta yadu ko ta bazu zuwa garuruwa na kusa ko na nesa, aiki ne wurjanjan.

Barkewar Annoba: A wannan mataki fa annoba ta zama ruwan dare-game-duniya kenan, wato ta zama ‘pandemic’ kenan a Turance. A nan abin zai shafi kasashen duniya da sannan kuma a wannan mawuyacin hali, annoba na gagara dakilewa ko shawo kai, har sai ta yi mummunar illa.

Idan annoba ta zama ‘pandemic’, to wanda ya kamu zai iya shafa wa wanda bai kamu ba cikin kankanin lokaci. Kuma duk wani kokarin da za a yi bayan ta barke, to sai ta ci rayuka da dama, ko kuma sai ta shiga jikin mutane masu yawan gaske.

A irin wannan matakin ne ake daukar matakai na gaggawa, masu tsauri kuma masu takurawa sosai, ta yadda za a yi kokarin shawo kan ta, bayan ta yi ko ta gama yin mummunar barna.

Share.

game da Author