CIWON KODA: Wayar da kan mutane da sawwake farashin magani zai rage yaduwar cutar

0

Kungiyoyin kare rajin dan adam da kungiyar likitocin koda sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta karfafa wayar da kan mutane hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar koda sannan ta samar da kula a farashi mai sauki domin hana yaduwar cutar a kasar nan.

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a taron ranar wayar da kan mutane kan cutar koda da ake yi ranar 12 ga watan Maris na kowacce shekara inda suke kokawa game da yadda cutar ke ta kara yaduwa a kasar nan.

Shugaban kungiyar Ifeoma Ulasi ta ce bincike ya nuna cewa akalla mutane miliyan 25 a Najeriya na fama da wannan cutar.

Ifeoma ta ce hakan na da nasaba da matsalolin rashin sani, rashin isassun asibitocin samun kula da tsadan farashin kula da ake fama da su a kasar nan.

Wani likitan koda dake asibitin FMC Birnin Kebbi jihar Kebbi Moses Tari ya koka da adadin yawan mutanen dake kwance a manyan asibitoci a Jihar Kebbi da kasar gaba daya.

Tari ya ce kusan kullum sai manya-manyan asibitoci a kasar nan sun samu maralafiya dauke da wannan cuta da aka turo asibitin domin a duba.

Ya ce rashin isassun asibitoci da rashin isassun kwararrun ma’aikata na cikin matsalolin dake haddasa haka a kasar nan.

Tari ya yi kira ga gwamnati da ta dauki isassu kuma kwararrun ma’aikata tare da gina asibitocin da za su kula da masu fama da wannan cutar a kasar nan.

Hanyoyin kamuwa da cutar koda

1. Yawan amfani da man dake canza kalan fatar mutum na kawo cutar a jikin mutum.

2. Yawan shan magungun musamman wadanda ake sha ba tare da izinin likita ba.

3. Rashin shan ruwa a lokacin da ya kamata.

4. Shan giya da zukar taba sigari.

5. Kamuwa d cutar kanjamau,Hepatitis.

6. Kamuwa da cutar hawanjini.

7. Kamuwa da cutar siga wato Diabetes.

8. Jin rauni a koda.

9. Kiba da rashin motsa jiki.

10. Shakan gurbatacen iska.

11. Yawan shan kayan zaki da cin gishiri.

Alamun cutar

Likitoci sun bayyana cewa cutar koda na daya daga cikin cututtukan da ba a iya gane alamun cutar sai lokacin da ya yi wa jikin mutum lahani.

Sun ce a wannan lokaci ne ake iya gane alamun cutar da suka hada da kumburin jiki da tafin hannu da kafaffuwa, yawan samun ciwon kai, yawan amai, rashin iya numfashi yadda ya kamata, rashin yin fitsari yadda ya kamata da sauran su.

Share.

game da Author