Mutane 144 sun mutu a sanadiyar kamuwa da Zazzabi Lassa a Najeriya

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa mutane 114 sun mutu a dalilin kamuwa da zazzabin lassa a Najeriya

An yi wannan rashe-rashe daga watan Janairu zuwa Maris 2020 a kananan hukumomi 119 dake jihohi 27 dake kasar nan.

An kuma kara samun wasu ma’aikatan kiwon lafiya biyu da suka mutu a dalilin kamuwa da cutar a jihohin Edo da Bauchi.

A lissafe dai adadin yawan ma’aikatan kiwon lafiya da suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris ya kai 29.

Kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya da suka hada da NMA da NARD sun yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali wajen daukan matakan kawar da cutar.

Kungiyoyin sun razana matuka a yadda cutar ke yawan kama ma’aikatan kiwon lafiya da yadda cutar ke yawam bullowa a duk shekara.

Sakamakon bincike ya nuna cewa jihohin Ebonyi, Taraba, Edo, Bauchi da Ondo na daga cikin jihohin da suka fi fama da cutar.

A jihar Edo mutane 288 sun kamu da cutar sannan 32 sun mutu, Ondo mutane 279 sun kamu da cutar inda 38 suka mutu.

A jihar Ebonyi 59 sun kamu da cutar 13 sun mutu,Taraba mutane 47 sun kamu wasu 17 sun mutu sannan a jihar Bauchi mutane 35 sun kamu kuma tara sun mutu.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne hukumar ta sanar cewa mutane 132 ne suka rasu a dalilin kamuwa da cutar

Share.

game da Author