Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Aljeriya ta sanar cewa mutum daya ya mutu a dalilin kamuwa da Coronavirus.
Ma’aikatar ta ce wata mata dake kwance a asibitin lardin Blida ta rasu ranar Alhamis.
A yanzu dai adadin yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar sun kai 24 sannan mutuwar wannan mata shine na farko tunda cutar ta bullo a kasar.
A ranar Talata kasar Morocco ta sanar cewa mutum daya ya mutu a dalilin cutar coronavirus kuma kasar Masar ta sanar da mutuwar mutum daya a kasar ranar Lahadi.
Kasashen Masar da Algeria ne suka fi fama da cutar a Nahiyar Afrika sannan a kasashen dake Kudu da Saharan Afrika kasar Afrika ta kudu ce ta fi samun yawan mutanen dake dauke da cutar.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta ce mutane 107 daga Nahiyar Afrika 12 na dauke da cutar.
Kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi fargaban bullowar cutar a Nahiyar Afrika inda suke cewa abin zai yi muni musamma yadda mazauna yankin ke yawan tafiya zuwa kasar Chana sannan da matsalar rashin ingantaccen fannin kiwon lafiya.
Sannan a ranar 11 ga watan Maris ne Hukumar Kiwon Lafiya ta duniya ta bayyana cewa cutar coronavirus ta zama annoba a duniya yanzu.
Shugaban hukumar Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa an ki ayyana cutar a matsayin annoba saboda kada a tada hankula da kuma tsorata mutane a duniya.