Bankin AfDB zai tallafa da lamunin dala bilyan 3 domin farfado da tattalin arziki Afrika

0

Bankin Bunkasa Afrika, wato Africa Development Bank, zai tallafa da zunzurutun kudi har dala bilyan 3 domin ceto kasashen Afrika da masana’antun nahuyar daga durkushewa sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus a duniya.

Wannan ne karon farko da AfDB zai tanadi wadannan makudan kudade masu yawa domin bayarwa ga wasu kasashe da manyan masana’antun hada-hadar kasuwanci na nahiyar.

AfDB ya ce zai samar da kudaden daga Babban Banki da sauran manyan cibiyoyin hada-hadar kudade, wadanda nankin zai bai wa kudin ruwan da bai kai kashi 1 bisa 100 ba.

“Cutar Coronavirus ta yi mummunar I’ll a ga tattalin arzikin duniya, ba ma ma Afrika kadai ba. Dalili kenan za mu Nada wadannan kudade a bisa sharadin tsawon shekaru uku domin a farfado da wasu kasashe da kuma masana’antun nahiyar.”

Shugaban Bangaren Bada Lamunin Tsarin CIB na Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, mai suna Tanguy Clagui ne ya yi wannan bayanin.

Coronavirus ta tsaida bunkasar tattalin arzikin duniya, yayin da kashi 80 bisa 100 ha hada-hadar masana’antu da kasuwanci a duniya suka yi tsaye cak.

Hakan ya biyo bayan akasaein ma’aikatan odisoshi, xibiyoyin hada-hada da kuma uwa uba ma’aikatan manyan masana’antun samar da abubuwa na duniya duk sun daina fita aiki saboda Coronavirus.

Akalla dai mutane 600,000 suka kamu a duniya, yayin da ta kashe mutum 25,000 ya zuwa karshen wannan mako.

A Afrika kuwa, sama da mutum 4,000 suka kamu da cutar Coronavirus.

Wannan tallafi na bankin AfDB ya zo daidai a lokacin da wasu hamsahakan attajirai musamman a Najeriya suka tashi tsaye wajen sanarwar bayar da tallafi ga gwamnati domin kokarin dakile Coronavirus, son kada ta yi mummunar barna irin yadda ta ke kan yi a Turai, Asiya da Amurka.

Share.

game da Author