CORONAVIRUS: Sai wanda kwanan sa ya kare ta ke kashewa – Fastor Adeboye

0

Shugaban Cocin RCCG, Enoch Adeboye, ya yi kira ga daukacin mabiyan sa a fadin duniyar nan cewa su daina fargaba da ranaza da cutar Coronavirus, domin sai wanda kwanan sa ya kare kadai ta ke kashewa.

“Ko da Coronavirus ko babu ita, idan kwanan ka ya kare za ka mutu. Don haka uta annobar Coronavirus wanda ajalin sa ya zo karshe ta ke kashewa. Kuma kushewar badi ai sai badi.”

Adebayo ya yi wannan jawabi ne a yau Lahadi kai-tsaye, ya na mai cewa bai ga dalilin da zai sa mutane su rika yin fargabar cutar Coronavirus ba.

Daga nan ya bayyana cewa ubangiji ya shaida masa cewa nan da wasu ‘yan kwanaki kadan cutar za ta tafi, a nsme ta sama ko kasa a rasa.

Faston ya yi wannan jawabi ne a lokacin da akalla sama da mutum 600,000 suka kamu da cutar a duniya, kuma ta kashe sama da mutum 25,000 a duniya.

A Najeriya mutum 97 suka kamu, mutum daya ya mutu, uku kuma sun warke daga cutar.

Cikin wadanda suka kamu har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, Nasir El-Rufai na Kaduna da wasu da dama.

Adebayo na daga sahun gaba na shugabannin addinai da ba su bi umarnin a rika yin kaffa-kaffa da kuma killace kai a gida ba.

Ko a ranar Lahadi da ta gabata, sai da ya gudanar da ibada a Cocin sa, abin da ya janyo masa tsangwama, iron wadda a yanzu ake wa Shugaban Kungiyar Izala na bangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, wanda ya bijire wa umarnin gwamnati, ya gudanar da sallar Juma’a a Jos.

Share.

game da Author