Fitaccen Dan kasuwa kuma attajiri, Aliko Dangote ya bayyana cewa Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi masa ya fito.
Sakamakon ya nuna Dangote ba ya dauke da cutar.
Shi da kansa ya rubuta a shafin sa ta tiwita inda ya ce tun bayan samun wasu da yayi mu’amula da da cutar ya Mika jinin sa domin a duba shi.
” Sakamakon ya nuna bani dauke da cutar.
Idan ba a manta ba, Dangote ya gana da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, da kuma Abba Kyari da dukkan su sun kamu da cutar.
Shi dai Allah yayi masa gyadar dogo.
Dangote da wasu attajiran Najeriya sun kafa gidauniya domin tallafa wa gwamnatin Najeriya game da yaki da Coronavirus da take yi.
Shima