‘Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun bindige mutane bakwai a Kaduna

0

Wasu ‘yan bindiga da aka tabbatar su na sanye da kayan sojoji sun bindige mutum bakwai, kuma sun jikkata wasu mutum biyar a tsakanin Kajuru da Karamar Hukumar Kachia, jihar Kaduna.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya tabbatar da wannan hari, kamar yadda ya bayyana a cikin wata takardar da ya sanar wa manema labarai a ranar Alhamis, a Kaduna.

Jalige ya ce an kai harin wajen karfe 7:15 na dare a ranar Alhamis.

“Wasu ‘yan bindiga ne dauke da manyan bindigogi, kuma sanye da kayan sojoji, suka kutsa tsakiyar kasuwar garin cikin mota.

“Sun rika bude wa mutane wuta, har suka kashe mutum bakwai su ka jikkata wasu biyar.

“An sanar wa DPO na Kajuru da na Kachia halin da ake ciki. Sun kuma gaggauta tura zaratan jami’an su a can. Amma dai kafin su karasa har ‘yan bindigar sun kashe mutum bakwai sun jikkata wasu biyar.”

Ya ce ‘yan sanda sun dauke gawarwakin wadanda aka kashe da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Kachia.

“ Gawarwaki na can dakin ajiye gawa, su kuma wadanda aka ji wa ciwo, an kwantar da su ana ci gaba da kula da samun lafiya da saukin su.

Jalige ya ce tuni hankula sun kwanta a yankin, jama’a na gudanar da harkokin su.

Ya sha alwashin za a gano wadanda suka yi wannan mummuna aiki.

Ya roki al’ummar yankin su taya jami’an tsaro sa-ido kan wani bakon-idon da ba a amince masa ba.

Jihar Kaduna na ci gaba da fama da hare-haren masu garkuwa da mutane sa kuma ‘yan bindiga da ke kashe-kashe, musamman a kudancin yankin da kuma yankin Karamar Hukumar Birnin Gwari.

Haka nan kan titin Abuja zuwa Kaduna ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane.

Share.

game da Author