Wani mutum ya kamu da cutar Coronavirus a kasar Algeria

0

Ma’aikatar kiwon lafiya, kidaya da gyara asibitoci na kasar Algeria ta sanar cewa wani matafiyi da ya shigo kasar daga kasar Italy ya kamu da cutar Coronavirus.

Ma’aikatar ta ce matafiyin ya shigo kasar Aljeriya ne ranar 17 ga watan Fabrairu.

An gano haka ne bayan gwajin cutar da aka yi wa wannan mutum. Sannan ma’aikatar ta sanar wa kungiyar kiwon lafiya ta duniya halin da suke ciki.

Algeria itace kasa ta biyu dake Nahiyar Afrika da wani ya kamu da cutar.

Baya ga haka WHO ta yi kira ga kasashen Afrika da su kara karfafa matakan hana shigowa da cutar a kasashen su ganin yadda wannan cuta ke ta kara yaduwa a kasashen duniya.

A yanzu haka cutar ta shiga kasashen duniya 30 sannan mutane sama da 2000 sun kamu da cutar a wadannan kasashe.

Kungiyar ta ce ta tallafawa wa wasu kasashen Afrika musamman wadanda ke ci gaba kuma da suka fi yawan tafiya zuwa kasar Chana da kayan gwaji domin ganin ta hana shagowa da cutar.

Wadannan kasashe kuwa sun hada da Masar, Algeria, Afrika ta Kudu, Najeriya, Ethiopia, Morocco, Sudan, Angola, Tanzania, Ghana, Kenya, Rwanda da Tunisia.

Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne aka samu tabbacin bullowar cutar CoronaVirus a nahiyar Afrika inda aka samu wani ya kamu da ita a kasar Masar, wato Egypt.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar, ta tabbatar a haka inda tace wani matafiyi ne da ya shigo kasar ya kamu da ita.

Ma’aikatar ta bayyana cewa tuni har an killace wannan matafiya a wani asibiti sannan an ci gaba da bincike domin kada cutar ta yadu.

Ma’aikatar ta ce tunda aka samu tabbacin kamuwar wannan cuta ta gaggauta sanar da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya domin a dauki matakin gaggawa

Share.

game da Author