ZAMBAR NAIRA BILYAN 1.5: EFCC ta cukumi tsohon Kakakin Majalisar Kano

0

Tsohon Kakakin Majalisar Kano, Isiyaku Ali Danja, ya fada hannun jami’an EFCC, a kan zargin yin rub-da-ciki da makudan kudaden ayyukan mazabu.

Kanakin Yada Labarai na EFCC, Tony Orilade ne ya fitar da sanarwar kamun Danja a ranar Laraba.

Ya ce an kama Danja bayan an gabatar da rubutaccen korafi a kan sa, bisa zargin karkatar da kudaden harajin da ya kamata gwamnatin Kano ta biya Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS).

Orilade ya ce an karkatar da sama da naira bilyan 1.5 daga wani karamin asusun gwamnatin jihar Kano.

An kama Isiyaku Danja, kwana biyu bayan damke Mukhtar Ishaq, Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Gwamnatin Jihar Kano, bisa tuhumar da ake masa ta wawurar naira milyan 86.

“ EFCC ta gano an rika karkatar da makudan kudade daga asusun gwamnatin Kano zuwa asusun wani kamfani mai suna Allad Drilling Limited, wanda shi Danja din ne shi kadai ke sa hannu a madadin shugaban kamfanin.”

Hakan kenan ya na nuna kamfanin na sa ne.

“ EFCC ta kuma gano cewa shi ne da kan sa ya rika zuwa ya na cire kudaden, kuma shi kadai ne zai iya gane ko an biya kudaden ayyukan ko a’a.
Hukumar ta ce za a gurfanar da shi da an kammala bincike.

Share.

game da Author