Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kamata ya yi shugaban kasa ya fito daga kudancin kasar nan a zabe mai zuwa na 2023.
Ya ce yin hakan zai kara karfafa dimokradiyya da kuma tsarin karba-karba a yankunan kasar nan.
Kafin shi, kwanan baya tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya bayyana irin wannan ra’ayin.
Shi Babangida ya fito karara ya ce a kudun ma a bai wa kabilar Igbo. Amma shi kuma El-Rufai bai fito ya ce a bai wa Igbo ko Yarabawa ba.
“Ittifakin da mutanen Najeriya suka yi shi ne shugabanci ya rika yin karba-karba tsakanin kudu da Arewa. Ba wai rubutacciyar doka ba ce, amma dai duk kowa ya fahimci hakan.” Inji El-Rufai.
El-Rufai ya ce a cikin PDP akwai wannan rubuce a matsayin doka, amma kuma a zaben 2015 suka karya ta.
“Yar’Adua ya ras ya na a kan mulki, wanda tilas Jonathan ne zai karasa wa’adin sa na shekaru hudu. Da zaben 2011 ya zo, sai wasu mutane da dama suka rika tayar da jijiyar wuya wai ba su yarda da Jonathan ya tsaya takara ba.
“Sun ce kamata ya yi Jonathan ya bari wani dan Arewa ya tsaya takara domin ya karasa wa’adin ‘Yar’adua na zango na biyu.
‘Na fito na ki amincewa da haka, na ce ai kaddara ce ta kai Jonathan a kan mulkin, don haka tunda ya na kai, kamata ya yi a bar shi a tsaya tsakara a zaben 2011.”
Daga nan ya ce duk da dai babu wata rubutacciyar yarjejeniyar karba-karba a APC, to ya kamata ‘yan Arewa su hakura bayan Buhari ya kammala shekaru takwas, a bai wad an kudu mulki.
Sai dai kuma wasu da dama cikin manyan APC daga Arewa, ba su so a bai wa dan kudu mulki bayan cikar wa’adin zangon Buhari biyu.