Kakakin majalisar Kaduna, Aminu Shagali yayi murabus, Zailani ya zama sabon Kakaki

0

Kakakin majalisar jihar Kaduna Aminu Shagali ya mika takardar yin murabus a zauren majalisar ranar Talata.

Honorabul Yusuf Zailani wanda shine mataimakin shugaban majalisa ya zama sabon shugaban majalisar jihar.

Rahotanni sun nuna cewa da yawa daga cikin ‘yan majalisar jihar sun yi wa Shagali bore inda suka tilasta masa da ko ya sauka daga kujeran shugaban majalisa ko kuma su tsige shi.

A ranar talata kuwa sai Shagali ya mika takardar yin murabus daga kujerar shugabancin majalisa.

Sabon Shugaban majalisa, Yusuf Zailani ya amince da nadin sa inda a ranar farko ya zauna a kujerar shugabancin majalisar.

Share.

game da Author