TA FARU TA KARE: Kotu ta kama Olisa Metuh da laifi

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kama tsohon Kakakin Yada Labarai na Jam’iyyar PDP, Olisa Metuh da laifin karbar kudi gwamnati.

An same shi da kamfanin sa mai suna Destra Investment Ltda a laifin karbar naira milyan 400 daga ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa na Lokacin Goodluck Jonathan, Samabo Dasuki.

Mai Shari’a ya ce Oliseh ya san cewa kudin gwamnati ne aka gabza aka ba shi, kuma ya kamata ya san cewa kudin laifi ne ya aikata karbar kudaden.

Ana zargin sa ne da aikata laifuka bakwai da suka hada da karkatar da kudaden da Sambo Dasuki ya ba shi.

Cikin watan Fabrairu, Metuh ya bayyana wa kotu cewa shi bai aikata laifin komai ba.

Sannan kuma an zarge shi da karbar dala milyan 2 wuri-na-gugar-wuri, kai-tsaye ba tare da bi ta banki ba.

A kokacin da ake rubuta wannan labarin, Mai Shari’a na ta kokarin hardada sauran laifukan caje-cajen da suka rage kafin a yanke hukuncin da zai hau kan Metuh.

Bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari, an kama mutane da yawa da aka zarga da karbar kudade a hannun Dasuki, ciki kuwa har da tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa, Musuliu Obanikoro da wasu da dama.

Yanzu kuma za a zura ido a ga irin hukuncin da za a yi wa sauran wadanda aka zarga da karbar kudade a hannun Dasuki.

A lokaci da aka kama Dasuki, an ce Jonathan ya bada umarni ne ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ya rika bayar da kudin. Kuma ya rika yi tun a zamanin Jonathan.

Metuh dai yace a matsayin sa jami’an yada labarai, an ba shi kudaden don ya yi ayyukan musamman da su, kuma ya yi.

Sai dai kuma har yau shi Gwamnan Babban Bankin ba a tuhume shi ba, sai ma kyale shi da aka yi ya ci gaba da rike CBN, kuma a cikin 2019 Buhari ya sake nada shi, bayan shekarun sa na shugabancin bankin sun cika.

Share.

game da Author