Gobara ya babbake gidan wani fitaccen likita a Maiduguri

0

Adaidai ana ci gaba da bukukuwar shiga sabuwar shekara ne a garin Maiduguri sai mai makon a yi farinciki da wannan rana sai kuma ya koma bakin ciki ga wani babban likita da ke aiki a hukumar kula da asibitoci na jihar Barno mr suna Dr Olugbenga Aina.

Wakilin PREMIUM TIMES da ya garzaya wannan wuri ya shaida cewa ko tsinke iyalan Aina basu iya fiddawa ba daga gidan domin kuwa kaf gidan ya kone kurmus.

A cewar wakilin mu, babu wanda ya ji ciwo a wannan gobara.

Daya daga cikin ya’yan Dr Aina ya ce har yanzu basu san sanadin wannan gobara ba domin su dai sun ga kawai gidansu yana babbakewa ne.

Abin tausayi a ciki kuma shine yadda shi mahaifin su Olugbenga Aina ma baya gida, yana can a garin Bama wajen aikace-aikacen duba marasa lafiya a sansanonin ‘yan gudun hijra dake can Bama.

Daga baya dai jami’an hukumar kashe gobara ta jihar sun kashe dan sauran burbudin wutan da ke ci a kangon gidan.

Share.

game da Author