Hukumar kula da aikin malunta ta jihar Kaduna ta bayyana cewa mutane sama da 14,000 ne suka rubuta jarabawar karshe na neman aikin malunta a jihar.
Shugaban hukumar Mary Ambi ta sanar da haka da take hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kaduna.
Ambi ta ce a lissafe dai gwamnati na bukatar akalla sabbin malamai 7,600 ne da zasu karantar a makarantun sakandaren jihar amma kuma mutane 62,000 ne suka rubuta jarabawar farko da aka yi.
“ Daga cikin mutanen da suka rubuta jarabawar akwai wadanda ke da satifiket din digirin digir-gir, wato Masters da Phd.
” Za mu tabbata wadanda suke da takardun da ya dace ne za mu dauka da wadanda cancanta su koyar da ‘ya’yan mu a makarantu.
Mary ta ce hukumar za ta aika da sunayen wadanda aka dauka nan ba da dadewa zuwa ga ma’aikatar ilmi ta jihar domin amincewa da su da kuma basu takardun daukan aiki.
An rubuta wannan jarabawa ne a watan Disambar 2019.
Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne Jami’ar Cibiyar ‘Global Partnership for Education (GPE)’ da ‘Teacher Professional Development (TPD)’ Halima Jumare ta bayyana cewa a cikin watanni biyu kacal gwamnatin jihar Kaduna ta horas da malamai da ma’aikatan makarantun firamare 5,834.
Halima ta ce an horas da wadannan malamai kan yadda za su iya karkato da hankulan dalibai ta hanyoyin dabam-dabam kamar ta wakoki da suran su.
Halima ta ce a yanzu haka wasu malamai 4,742 na samun irin wannan horo bayan 5,834 din da aka fara horaswa.