Idan kai ne aka ba ka kyautar naira milyan biyu, a matsayin ‘Barka-da-Sallah’ me za ka ce? Godiya z aka yi ko kuwa rainawa z aka yi? To wannan amsa dai ba wata mai wahala ba ce idan kai Sanata ne. Domin cewa za ka yi: “Sun yi min kadan.”
To ai kuwa hakan ya faru, domin wasu sanatocin ma cewa suka – ai wannan kyautar “cikin-cokali ce, ba cikin-kandami ba”, idan aka kwatanta da dimbin kudaden da suke kashewa a lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Wasu daga cikin su ma cewa suka yi da zarar sun koma Majalisa daga hutun karshen shekara, to za su tayar-da-balli kawai.
“Yanzu kamar mu a dube mu a bai wa kowa naira milyan biyu a lokacin Kirsimeti, to me za ta yi mana. Za mu yi gungu mu je mu samu Shugaban Majalisar Dattawa mu kai masa kukan mu.”
A ranar 18 Ga Disamba, 2019 ne aka raba wa kowanen su, Kirista da Musulmi naira milyan biyu a matsayin kudin shagalin bukukuwan Kirsimeti da hutun karshen shekara.
Ba a hannu aka damka musu kudaden ba.
Kowa tura masa aka yi ta asusun ajiyar sa na banki. PREMIUM TIMES ta ga ‘alat’, wato alamun shigar kudi na wasu sanatoci biyu.
Wannan kuwa ya nuna cewa kowanen su an tura masa naira milyan biyu din kenan.
Bayanan ‘alat’ din bai nuna ga kudin ko na mene ne ba. Amma dai kowa ya sani cewa idan ya ga wadannan kudade, to goron-bukin Kirsimeti nne aka tura musu.
Sai dai kuma maimakon su yi godiya da murna, sai dukkan su suke ta korafi da guna-guni, har wasu da dama daga cikin su na barazanar yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan takakkiya.
Wani hasalallen Sanata cewa ya yi: “An ce masa mu yi amfani da kudin domin yi wa iyalan mu cefane da kuma bayar da ihisani ga mazabun mu. To ni dai tsaye kawai na yi sororo, ban ma san abin da zan ce ba, tsawon mintina da dama.”
Daga nan sai wannan sanata ya bayyana cewa shi Sanata Ahmad Lawan ya kasa fahimtar irin nauyin da ke hawa kan sanatoci, a duk lokacin da suka je ganin-gida a yankunan mazabun su.
“Akwai kananan hukumomi da yawa a karkashin mazaba ta. Ya ma zann iya tunkarar sun a ce da guzirin naira milyan daya kacal na je musu? Ai ba ma zai yiwu ba,”
“Kai ni fa idan ina so na shafa wa kai na lafiya, to idan zan je wani taro ko halartar biki a mazaba ta, akalla sai na yi guzirin naira milyan 50.” Inji sanatan wanda bai so a ambaci sunan sa.
“Tun bayan wata daya kenan, ba mu samun abin kirki, sai dai a dan rika damka mana a hannu. Mun bai wa gwamnati goyon bayan samun nasara, ga shi kuma jama’a sai habaici suke mana, wai ba mu komai, mun zama ’yan-amshin Shata.”
Zargin yankan-baya
Wasu sanatocin na ganin cewa watakila ma kudaden da ya kamata a ba su sun wuce naira milyan, amma wasu ne suka zabtare kudaden. Shi ya sa inji shi, aka ki bayyana wa kowa abin da zai samu, sai dai aka ce ya jira zai ji ‘alat’.
“Kai ni fa mamakin da na fi yi shi ne irin makudan kudaden kasafin kudi da ake tura wa Majalisar Dattawa. Idan na kwatanta da dan cikin-cokalin da ake gutsira mana kamar wasu mabarata, abin ya na ban i makaki kwarai.
“Abin takaicin kuma mu ba kamar Shugaban Majalisa ba ne, wanda ya ke da ikon tafiya a jirgin gwamnati da kuma shan fetur kyauta a motocin sa, a duk inda zai tafi.”
Majalisar Dattawa na karbar makudan kudade a duk shekara, duk kuwa da cewa sama da ‘yan Najeriya milyan 90 na cikin radadin kuncin fatara da talauci.
Discussion about this post