Hukumar Kwastan Reshen Jihar Sokoto ta bada sanarwar damke katan 640 na maganin karfin maza, wanda kudin sa zai kai naira milyan 914.8.
Kakakin Kwastan na Jihar Sokoto, Magaji Mailafiya, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewa an kama wannan magani da ake kira Mai Bindiga, wato “AK47” a kan iyakar Illela da Kware a ranar 24 Ga Nuwamba, 24.
Mailafiya ya kara da cewa dukkan wadannan magunguna na haramtacciyar hanyar sumogal ce, domin gwamnati ba ta bayar da iznin a rika shigo da su cikin Najeriya ba.
Haka nan kuma sun bada sanarwar kama wasu motoci kirar Toyota Carina ll guda uku dauke da jarkokin man girki 132, katan 85 na batir mai kan damisa. Sai kuma katan 86 na magi kafi-zabo a yankin Achida da Goronyo.
Har ila yau, Hukumar Kwastan din ta Sokoto ta sanar da kama buhuna da aka cika da adduna guda 800 a ranar 20 Ga Nuwamba.
Daga nan sai sanarwar ta yi kira ga jama’a da su rungumi halastacciyar hanyar da gwamnati ta amince a rika yin harkokin kasuwanci, ba hanyar fas-kwauri ba.
Rundunar ta sha alwashin ci gaba da tashi tsaye domin dalike harkokin fas-kwauri a yankin da ta ke da ikon hana wannan makauniyar sana’a.
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta rufe kan iyakokin kasar nan ne dai ake ci gaba da kama kayan sumogal masu yawan gaske da ake shigowa da su ta barauniyar hanya.