RIKICI YA BARKE A FADAR SHUGABAN KASA: Aisha Buhari ta ragargaji Garba Shehu, Mamman Daura

0

Uwargidan shugaban Kasa, Aisha Buhari ta ragargaji kakakin fadar gwamnati Garba Shehu inda ta bayyana cewa wasu jiga-jigan makusantan Buhari na ingiza shi ya ci mata mutunci.

Aisha ta fitar da wannan sako ne ga ‘yan Najeriya don su sani cewa akwai wasu umarni da wasu ke bada wa wanda da ba da sani Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ke fidda su ba.

Ta ce Garba Shehu ya zama dan sakon su sai yadda suke so yake yi maimakon aikin kare shugaban kasa da iyalansa.

” Tuni dai Garba Shehu ya koma yana yi wa wasu aiki da basu tabuka komai ba a wannan tafiya da ake ciki. Ya koma kacokan sai yadda suke so yake musu, ba shugaba Buhari ba.

” Ba kawai ayyukan gwamnati ba, ya kai ga har shisshigi yake ga harkokin cikin gidan shugaba Buhari domin kawai ya biya wa wadannan bukatun su.

” Idan baku manta ba shi gogan dake shirya wannan makininitar, ( Mamman Daura) ya kama wa kansa gida a Aso Rock, bayan shekara hudu, mai makon ya fice salin-alin sai kawai suka shirya da ‘yar sa Fatima ta rika daukar abubuwan dake faruwa a bidiyo ta yada wa duniya don a ci mini mutunci.

” Garba Shehu, bai fito ya fayyace wa duniya gaskiyar maganar ba duk da ya san komai saboda abin ya shafi iyayen gidan sa ne sai bai ce komai ba. Sai da na dawo da kai na sannan na fayyace wa duniya ainihin abinda ya auku.

Sannnan kuma shi Garba Shehu dinne da kansa ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa wai shugaban kasa ya soke ofishin Uwargidan shugaban kasa. Sai daga baya ya sanar wa wani hadimi na cewa wai Mamman Daura ne ya unarce shi ya sanarda haka ba Buhari ba.

Aisha ta ce kamata yayi Garba Shehu yayi murabus kawai idan da ya san ciwon kansa amm da yake wasu yake wa aiki. Sannan uma ta koka kan yadda Garba Shehu ya ruka azazzalawa lallai sai an dakatar da hadimai ta. Wadda daga baya hakan aka yi.

Share.

game da Author