Sai fa gwamnati ta yi karin haraji sannan za ta iya biyan ayyukan gina titina – Fashola

0

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa manyan ‘yan kwangilolin ginin titinan gwamnatin tarayya na bin gwamnati bashin naira bilyan 306, don haka sai an yi karin harajin VAT sannan gwamnati za ta iya biyan ayyukan gina titina.

Haka kuma Fashola a cikin bayanin na sa, ya kare dalilin da ke tilasta gwamnati ciwo bashi domin yin ayyuka.

Fashola ya yi magana ce bayan da Daily Trust ta buga labarin cewa gwamnati ta kashe naira tiriliyan 1.5 a wannan shekarar wajen biyan kudin tallafin man fetur, da aka fi sani da ‘subsidy’.

Minista Fashola ya ce gaba daya ma daga shekarar 2015 har zuwa karshen 2018 Ma’aikatar sa ba ta karbi naira tiriliyan 1 daga gwamnatin tarayya ba.

Hakan inji shi, ya nuna irin karancin kudaden da gwamnati ke kashewa idan aka kwatanta da makudan da ta ke kashewa wajen biyan kudin tallafin mai.

Da ya ke bayani a lokacin da Shugabannin Kungiyar Masu Motocin Sufuri ta Najeriya ta kai masa ziyara a ofishin sa, Fashola yace, “Idan da a ce zan samu naira tiriliyan daya da za a kashe wajen gina titinan kasar nan, ai da an ga ayyuka tukuru.

“Amma ya zuwa watan Oktoba da ya wuce, ‘yan kwangila bin bashin naira bilyan 306 na titinan da suka yi aiki ba a biya su ba. Kuma na san wasu ma ba su kai ga kawo lissafin na su kudaden da muka rike musu ba mu kai ga biya ba.

“To duk fa abin nan mu har yanzu a wannan ma’aikatar, naira bilyan 73 kacal mu ka karba daga hannun gwamnatin tarayya.” Inji Fashola.

A kan wadannan dalilan ne Fashola ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati ta kara harajin VAT da harajin biyan kudin shingayen kan titi na ‘tollgates’ da za a fara karba a hannun direbobi nan gaba.

“Wasu mutanen ma cewa suke yi don me gwamnati za ta rika fita na ciwo bashi. To ina ganin ya kamata irin ku din nan ku fara fitowa kun a bayyana matsayar ku.”

Share.

game da Author