An cafke Kasurgumin mai fataucin miyagun kwayoyi a Minna

0

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Neja ta damke wani mutum dauke da buhunan ganyen WiWi da ya Kai kilo gram 1,072 a karamar hukumar Makowa.

Kwamandan hukumar Sylvia Egwunwoke ta sanar da haka da take zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna.

Egwunwoke ta ce shekarun wannan mutum su kama 56 sannan Dan asalin kauyen Bangi ne, dake karamar hukumar Mariga.

A baya an taba kama wannan mutum a Sakkwato Yana safarar ganyen WiWi.

Egwunwoke ta yi kira ga mutane da su hada hannu da hukumar domin a rika kama irin wadannan miyagun ayyuka.

Hukumar NDLEA ta yi kira ga sarakuna da malaman addinai da su rika fadakar da mutane da Kuma ja musu kunne game da illolin da me tattare da ta’ammali da muggan kwayoyi.

Idan ba a manta ba a watan Oktoba hukumar NDLEA ta cafke masu safarar miyagun kwayoyi har 15 tsakanin watannin Janairu zuwa Satumba a jihar Gombe.

Shugaban hukumar Aliyu Adole yace hukumar ta kama wadannan mutane ne da kilogram 523.174 na miyagun kwayoyi wanda a ciki akwai ganyen wiwi.

Share.

game da Author