Dan wasan kwallon kafa na Barcelona kuma dan kasar Argentina, Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ya fi shahara a 2019, wato Ballon d’Or.
A shekarar 2019 Messi ya zura wa kungiyarsa ta Barcelona da kasar sa kwallaye 46.
Messi ya yi nasara akan ‘yan wasa, Virgil van Dijk da Cristiano Ronaldo, wadanda suka zo na biyu da uku.
Idan ba a manta ba Messi ya taba lashe kyautar har sau biyar, wannan shine karo na shida da yake cira tuta.
Messi ya lashe kyautar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.
Yanzu aiki ja ne a gaban yan wasan kwallon kafa domin ga dukkan alamu idan ba birki aka taka wa Messi ba badi ma shine zai lashe wannan kyauta.
Discussion about this post