SHAWARA: Mutane 29 sun rasu a jihar Bauchi

0

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Bauchi Rilwanu Mohammed ya ce akalla mutane 29 ne suka rasu a dalilin kamuwa da cutar shawara a jihar.

Mohammed ya fadi haka ne wa manema labarai a garin Bauchi ranar Alhamis.

“ cutar ta bullo ne a kananan hukumomin Alkaleri,Bauchi,Darazo da Ningi.

“Akalla mutane 224 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 29 suka rasu.

Mohammed ya gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin dakile yaduwar cutar musamman ta hanyar yin allurar rigakafin cutar a wuraren da cutar suka fi bullowa.

“A yanzu haka mun yi wa mutane 500 allurar rigakafi a karamar hukumar Alkaleri sannan muna jiran gwamnati ta bamu magunguna rigakafi 600 domin mu yi wa mutanen dake karamar hukumar Ningi.

Mohammed ya yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da basu jin dadin jikinsu ba.

Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne aka ruwaito cewa mutane 10 daga karamar hukumar Ningi suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.

An gano wadannan mutane ne daga kayukan Tipchi, Deru, Sabon Gari, Tudun Wada da Barawo.

Ma’aikatan asibitin karamar hukumar da mai unguwar kauyen Tipchi Iliya Mohammed su yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo musu dauki domin hana yaduwar cutar.

Share.

game da Author