Fadar shugaban kasa ta tabbatar da rage ma’aikatan dake karkashin ofishin Buhari da Osinbajo

0

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da rage yawan ma’aikatan da ke aiki a ofisoshin shugaba Muhammadu Buhari da na mataimakinsa Yemi Osinbajo.

A wata takarda da ta fito daga fadar shugaba Buhari wanda kakakin Buhari Garba Shehu ya saka wa hannu ya tabbatar da wannan garambawul da ake yi a fadar gwamnati.

Sai dai kuma fadar ta karyata yadawa da ake ta yi a kafafen yada labarai cewa wai Buhari ya na wa mataimakinsa Osinbajo bita-da-kulli.

A takardar, fadar ta kara da cewa idan da za a lura, tun bayan rantsar da gwamnati a karo ta biyu aka fara rage masu taimakawa shugaban kasa da mataimakinsa.

Buhari ya ce gwamnati ta yi hakane domin ta rage yawan ma’aikatan da basu da wani amfani ko kuma an nadasu ne saboda buri ta siyasa.

Wannan shine babban dalilin da yasa aka zaftare wasu da dama ba kawai wadanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa ba har da na ofishin Buhari.

Sanarwan ta yi kira ga kafafen yada labarai da su rika tantance gaskiyar labaran su kafin su yada. Ya ce ba daidai bane arika cewa wai Buhari da mataimakinsa basu shiri suna yi wa juna takun saka ko kuma Buhari na yi masa tsangwama.

An rika yadawa a kafafen yada labarai cewa Buhari ya zaftare wa mataimakin sa hadimai saboda rashin jituwa da ya ke tsakaninsu da kuma yi masa tsangwama.

Wannan labari ya karade kasar inda masu sharhi da fashin baki a harkar siyasa ke cewa shugaba Buhari bai kyauta wa mataimakin sa ba wajen zaftare masa yawan hadimai.

Shehu yace gwamnati za ta ci gaba da yin haka domin rage yawan kudade da gwamnati ke kashe wa na babu gaira babu dalili.

Share.

game da Author