SAKAMAKON ZABEN KOGI: Yadda wani dan jagaliyar PDP ya dangwala kuri’a fiye da sau daya a mazabar dan takara

0

Wakilin PREMIUM TIMES ya kama wani mai goyon PDP ya na dangwala kuri’a fiye da sau daya, a mazabar dan takarar gwamna na PDP, Musa Wada.

Wada shi kuma ya kada ta sa kuri’ar a rumfar zabe ta PU 001, ta Mazabar Odu-Ogbeyaga a cikin Karamar Hukumar Dekina, wajen karfe 10:15.

Har zuwa wajen karfe 12:30 dan takarar gwamnan na PDP ya na rumfar da jefa kuri’a din ya na kallon yadda zabe ke gudana tare da magoya bayan sa.

Jim kadan bayan da ya kada kuri’ar sa, wada ya yi tattaunawa ta musamman da PREMIUM TIMES, inda ya yi zargin cewa ‘yan jagaliyar APC na kokarin kwace akwatinan zabe.

Ya ce jami’an tsaro da wasu matasan garin sun fatattaki ‘yan dabar da suka zo da nufin arcewa da akwatinan zabe.

Sai dai kuma wakilinmu ya ga wani mai goyon bayan gwamnan ya dangwala kuri’a akan akalla kuri’a guda 50.

Ya dangwala kuri’un ne a kan teburin wasu jami’an zabe, kuma a kan idon ‘yan sanda da jami’an ‘civil defence’.

Sai kuma wani da suke tare ya rika ce wa mai dangwala kuri’un ya yi hanzari ya gama, domin sun a so ne su dangwala wa guda 400.

Dama kuma tun kafin ya fara wannan dangwalen, wakilinmu ya ga wani ejan na wata jam’iyya ya na magana da jami’in INEC, Samuel Imoukhuede a fusace.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi Moukhuede, y ace ejan din ya fusata da shi ne, saboda ya ki ba shi hadin kai ya yi magudi.

Share.

game da Author