Sakamakon da ke ci gaba da fitowa daya bayan daya daga mazabu ko rumfunan zabe, su na ci gaba da nuna cewa PDP ta kamo hanyar kwance wa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi zani a tsakiyar kasuwa.
Dauk da cewa ya dan tabuka sosai a wasu rumfunan zabe, sannan kuma ba a san yadda dimbin sakamakon da za a ci gaba da fitarwa zai kasance ba. Amma dubi da yadda ake samun rata mai tsananin yawa, hakan na nuni da cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, to kwanaki kadan suka rage wa Yahaya Bello kafin ya kammala wa’adin sa a Gidan Lugard, wato fadar Gwamnatin Jihar Kogi.
Sakamakon da ya fito daga Mazabar Opulogba Randabawul, a Karamar Hukumar Ankpa, ya nuna cewa APC ta samu 94, ita kuwa PDP ta lashe 318.
Sai kuma sakamakon wata Mazaba ta Okene, inda Gwamna Bello yayi mai-shal, ya lashe dukkan kuri’u 340, yayin da PDP ba ta samu ko daya ba.
A Karamar Hukumar Ankpa, Mazabar Otupko, kusa da mayanka, APC ta samu 46, yayin da PDP ta samu 253.
A Yagba ta Gabas kuma a Mazbar Makutu, APC ta samu 98, ita kuma PDP ta na da 223.
Sakamakon da aka fitar daga Karamar Idah na Rumfar Zabe ta 4, PU10, PDP na da kuri’u 205, APC kuwa 17.
Haka kuma sakamako masu yawa sun kara fitowa daga garin Okene, babban birnin jihar, inda su ka nuna PDP na jan ragama, ko da ya ke akwai inda Bello ya lashe kuri’u da dama shi ma.
Har yanzu dai ba mu kawo maku rahotannin sakamakon zabe daga Karamar Hukumar Dekina ba, karamar hukumar da ta fi saura yawan masu jefa kuri’a, kuma mahaifar dan takarar PDP, Musa Wada.
A wannan karamar hukuma ce PDP ta fi yin kaka-gida.