Jami’an Kwastam sun kama kwantenoni 32 cike makil da lalatacciyar shinkafa

0

Hukumar Kwastam ta kama wasu kwantenoni har 32 cike makil da buhunan lalataccen shinkafa.

An kama wadannan kwantenoni ne a daidai ana kokarin shigowa da su kasuwannin Najeriya.

Kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana a lokacin da yake duba wadannan kwantenoni ya ce an shigo da shinkafan daga kasashen Thailand da Chana ne.

Ali yace Shinkafar bata da kyau yana mai cewa duk ta lalace wato lokacin da ya kamata ace an cinye shinkafar ya wuce tuntuni.

Bayannan kuma Ali ya ce a cikin kwantenonin an ga sabbin buhuna da aka buga musu sabon hatimi da ranakun kare aiki dabam.

” A cikin wadannan buhuna ne na ke kyautata zaton za a duddura wannan shinkafa domin saida su ga mutane a kasuwanni.

Share.

game da Author