2020: Buhari da Osinbajo za su cinye naira bilyan 3.5 a abinci da tafiye-tafiye

0

Ta tabbata cewa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo za su kashe har naira bilyan 3.5 wajen shagalin abinci da abin sha da kuma tafiye-tafiye a cikin shekara mai zuwa ta 2020.

Wannan adadin kudade masu tarin yawa da za su kashe kuwa ya nunka adadin wanda suka kashe a 2019.

Cikin shekarar 2019 dai sun kashe naira bilyan 1.4. Wannan adadin kudi masu tarin yawa da Buhari da Osinbajo za su kashe, lamarin ya zo da ban-mamaki, domin Buhari da kan sa ya koka dangane da yawan tafiye-tafiyen da ministocin sa da sauran manyan jami’an gwamnatin sa ke yi zuwa kasashen waje.

Dalili kenan ma ya bada umarnin hana su fita in dai ba da wani kwakkwaran dalilin da idan fitar ta kama, to za ta amfani kasa baki daya ba.

Cikin wannan kasafi na 2020, Buhari ya nemi Majalisa ta amince ya kashe naira bilyan 2.5 a tafiye-tafiye kasashen waje. Wadannan kudade sun hada har da wanda ofishin Mataimakin Shugaban Kasa zai kashe.

Jama’a da dama na ganin cewa tafiya kasashen ketare sun zame wa Buhari jiki, ganin cewa daga sake rantsar da shi ranar 29 Ga Mayu, ya fita kusan sau biyar kenan.

Tafiyar sa kasar Saudiyya jiya Litinin, ita ce ziyarar sa ta uku kasar a cikin watanni biyar kacal. Daga can kuma zai zarce kasar Ingila, sai ranar 17 Ga Nuwamba zai dawo Najeriya.

Zai kashe naira milyan 775 wajen tafiye-tafiye cikin Najeriya. Wannan kuwa za a iya yin la’akari da cewa tun da Buhari ya hau mulki, ko tafiya zuwa Kaduna bai kara yi a mota ba, daga Abuja.

Lissafi da kididdiga sun nuna cewa a gidan Buhari za a rika dafa abincin naira dubu 68,000 a kowace rana.

Wannan ya zo daidai da lokacin da Ministan Harkokin Noma da Inganta Rayuwar Mazauna Karkara, Sabo Nanono ya ce talaka zai iya cin abincin naira 30 a zama daya, ka ma ya ci har cikin sa ya cika fal.

A bangaren tafiye-tafiye an samun karin naira milyan 250 a hangaren Buhari. Haka kuma a bangaren abinci, za a ci na naira milyan 98 kenan a shekara.

Sai kuma lemo da sauran kayan shaye-shaye da tsotse-tsotse, tande-tande da lashe-lashe, Buhari zai tandi naira milyan 25.

Share.

game da Author