Bani da hannun jari a Kamfani wutan lantarki na KAEDCO – Namadi Sambo

0

Tsohon mataimakin shugaban Kasa Namadi Sambo ya bayyana cewa sam bashi hannun jari a kamfanin wutan lantarki na KAEDCO.

Namadi ya yi wannan zafafan kalamai ne don karyata jaridar Daily Post da ta buga labarin wai yana da hannu jari a kamfanin wutan lantarki na KAEDCO.

A takardar da ya fitar sannan ya saka wa hannu da kansa, Namadi ya karyata wannan magana sannan yayi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan magana cewa babu gaskiya a cikin sa.

” Ko a lokacin da na shugabanci kwamitin saida kadarorin kasa a lokacin da nake mataimakin shugaban kasa, mun yi aiki ne cikin tsoron Allah da ci gaban kasa. Kuma kowa ya shaida kuma an yaba.

” Lallai wannan jarida da ta buga wannan shirgegen karya ba ta yi min adalci ba. A dalilin haka ina kira ga editan jaridar da su gaggauta rubuta takardar bani hakuri da janye wannan labari nan da mako daya.

A karshe ya yi kira ga gdajen yada labarai da su rika tantance labarai kafin su wallafa su a koda yaushe don gudun yada karerayi.

Share.

game da Author