Abin da ya hana sojoji murkushe Boko Haram –Kwamanda

0

An bayyana rashin helikwaftocin yaki ga sojojin kasa ne babbar matsalar da ta hana sojojin Najeriya murkushe Boko Haram kwata-kwata.

Su dai sojojin kasa su na dogara ne da sojojin saman da ke amfani da jiragen yaki na sojan sama, a duk lokacin da za a kai wa Boko Haram hari ta sama.

Babban Kwamandan ‘Operation Lafiya Dole’, Manjo Janar Olusegun Adeniyi ne ya bayyana haka, jiya Alhamis, a lokacin da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Al’amurran Sojoji suka kai ziyarar gani da ido a Maiduguri.

Tawagar na karkashin jagorancin shugaban kwamitin, Sanata Ali Ndume, wanda ya ce sun kai ziyarar ce ta kwanaki biyu, domin su gane wa idon su halin da ake ciki.

Manjo Janar Adeniyi dai ya karbi jagorancin Kwamandan Gumurzun Yaki ne a cikin watanni biyu da suka gabata.

Adeniyi ya ce “tun farko Boko Haram fa ba su taba zama wata babbar barazana ko wani gungun masu karfi ba, kamar yadda ake tunanin su ke. “Abin da kawai sojoji ke bukatar a ba su domin su kakkabe Boko Haram kwata-kwata su ne hilikwaftoci na yaki, wadanda za su rika kai hari da su.”

“Akwai wata dabarar da za a yi amfani da ita domin a kakkabe su gaba daya. Sojoji na bukatar helikwaftoci na yaki domin su karasa da Boko Haram. Idan mu ka same su, shikenan. Saboda manyan jiragen yaki, su jets sun fa yi girma a yaki da ‘yan sunkuru.

“Tasirin helikwaftocin idan mu ka same su, to duk inda mu ke su nan wurin. Mu rika kwana tare da su kuma mu tashi a cikin su, haka manyan bindigogin da za a yi amfani da su, duk mu na tare da su.

“Na san cewa an dade shekaru ana ta kokarin kawo mana su. To tabbas da an wadata mu da su, Boko Haram zai zama tarihi kawai.”

Duk da cewa Boko Haram sun kashe dubban jama’a a shekarun baya, Adeniyi ya jajirce cewa Boko Haram ba wani marga-margan karfi gare su ba.

“Su fa Boko Haram ba karfi gare su sosai ba. Boko Haram ba su ma iya jure minti 15 ana zabarin wuta da su. Taron yuyuyu ne.

“Saboda na yi yaki da su gaba-da-gaba a Marte, Delta da Gubio, a lokacin da na mataimakin kwamanda da kuma lokacin da yanzu na ke kwamanda.”

Daga nan sai ya ce wa sanatocin, “ina rokon ku idan kun je Abuja, ku sanar cewa Boko Haram fa ba wata tsiya ba ce, ‘yan samame ne kawai.”

Adeniyi ya yi magana mai tsawo a kan muhimmancin sojojin kasa su samu helikwafta na su na kan su. Ba wai a rika dogara da jiragen yakin sojojin sama ba.

“Sojojin sama na yin kokari sosai da sosai. To amma fa akwai nisa daga inda suke.”

Sanatocin dai sun ganawar sirri da Adeniyi da kuma mataimakn sa har tsawon sa’o’i uku. Sun kuma gana da wasu sojojin da ke bakin daga.

Bayan kammala taron, Ndume da mataimakin sa Sanata Abdulrazak Namdas sun bayyana wa manema labarai cewa sun gamsu da irin kuzari da kuma yadda sojoji ke kishin gudanar da aikin su.

Ya ce sun je Jihar Borno ne domin su ga irin ci gaban da sojoji ke samu da kuma irin kalubalen da suke fuskanta.

Share.

game da Author