A ranar Alhamis ne dakarun sojojin Najeriya suka fatattaki wasu mahara da suka far wa gonar tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmad Yarima.
A arangamar da suka yi dakarun sun kashe mahara sama da 100 inda sojoji biyar suka rasu sannan wasu guda hudu suka ji rauni.
Wannan tashin hankalin ya auku ne a karamar hukumar Bakura dake jihar Zamfara inda a nan ne gonar yake.
Wasu mazaunan karamar hukumar sun bayyana cewa akalla mahara 200 dauke da bindigogi ne suka far wa wannan gona inda suka kashe masu gadin gonar guda biyu nan take.
“Muna ganin su sai muka gaggauta kiran sojoji inda bayan barin wutan da suka yi a tsakanin su akalla mahara sama da 100 ne suka sheka lahira a wannan arangama. Su kuma sojoji biyar suka rasu.
Bayan haka kakakin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ a jihar Zamfara Oni Orisan ya tabbatar da aukuwar haka kuma ya ce har yanzu ana gudanar da abincike akai.
Idan ba a manta ba a watan Satumba ne sulhun da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi da ‘yan bindiga masu garkuwa da kai hare-hare, ya sa aka saki mutane 372 da aka yi garkuwa da su.
An kuma samu adadin ‘yan bindiga 240 wadanda suka mika makaman su tare da tuba daga aikata mugayen halaye.