Zamu samar wa ‘yan Kasar Afrika ta Kudu tsaro a Abuja – Minista Bello

0

Ministan babban birnin Tarayya, Mohammed Bello ya yi kira ga mutanen Abuja da su yi hakuri bisa abubuwan da ya faru a kasar Afrika ta kudu kada su farwa kamfanonin ‘yan kasar.

Minista Bello ya ce ‘yan Kasar Afrika Ta kudu da ke zama a Abuja su ci gaba da zamnsu yana mai cewa gwamnati zata samarmusu da tsaro yadda ya kamata.

Daga nan sai ya roki matasa da sauran mutane da su yi hakuri sau daina farautar kamfanonin ‘yan kasar Afrika ta Kudu din cewa da yawa daga ciki duk hadin guiwa ne da attajiran Najeriya.

” Idan aka bari aka ci gaba da haka, zai durkusar da tattalin arzikin kasa ganin cewa mutane da dama suna aiki a wannan wuraren kuma duk ‘yan Najeriya ne.

Ya kara da cewa an aika da jami’an tsaro da dama domin samarda da tsaro a wurare da dama domin samar da tsaro a wadannan wurare.

Idan ba a manta ba, cikin daren jiya ne a jihar Legas, hasalallun matasa suka far wa babban shagunan Shoprite dake Abuja, inda suka yi warwasun kayayyakin masarufi, tabijin, kayan sawa, radiyoyi, wayoyi da duk wani abu da mutum zai iya dafe wa.

‘Yan kasar Afrika Ta Kudu sun dade sun farautar baki a kasar. Suna cewa wai sune suka zo kasar suka kwace musu aikin da ya kamata ace sune suke yi.

Abin dai ya kazanta ne a ‘yan kwanakin nan inda suke bi gida-gida, shago-shago suna buge duk wani da ban asalin dan kasar bane.

Wannan abu dai ya harzuka shugabannin kasashe da dama inda aka yi tir da wannan abu da suke yi.

Share.

game da Author