Gwamnatin Kaduna ta haramta kafa shigen ‘yan sanda a manyan titunan Kaduna-Abuja, Kaduna-Zaria, Kaduna-Birnin Gwari
Kwamishinan tsaron cikin gida da tsare-tsare na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana haka yana mai cewa daga yanzu duk wani shinge na ‘yan sanda ko Sojoji a manyan titunan Kaduna-Abuja, Kaduna-Zaria, Kaduna-Birnin Gwari ya haramta.
Aruwan ya ce daga yanzu duk shingen da jami’an tsaro suka kafa a wannan tituna karya doka ne.
Sannan yayi kira ga matafiya da su sanar da gwamnati duk inda suka ga irin haka domin ya haramta.
Tutunan Kaduna-Abuja, Kaduna-Zaria, Kaduna-Birnin Gwari sun yi kazamin suna wajen hare-hare, Fashi da Makami da kuma garkuwa da mutane.