Wani abun tashin hankali da tsoro da ya fadawa daliban Kwalejin Ilimi dake Waka-Biu Karamar Hukumar Biu, jihar Barno shine ganin yadda wasu daliban makarantar suka rika mutuwa bayan sun dawo daga yawon bude ido a wurin shakatawa dake Yankari.
Akalla mutane hudu ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya sannan wasu dalibai 12 na kwance a asibiti a na duba su.
Kamar yadda bayanai suka nuna, su dai wadannan dalibai sun fara nuna alamun rashin lafiya ne tun bayan da suka dawo daga Yankari.
Daya daga cikin wadanda suka rasu sun hada da ‘yan shugaban karamar hukumar Biu da ita ma ta tafi wannan ziyara.
An ce tun bayan dawowar su sai kawai mutum ya fara aman jini, daga nan shi kenan kuma kafin a gane ko menene sai ya cika.
Mutane hudu ne zuwa yanzu suka rasu.
Shugaban Kwalejin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan ba shi bane karo na farko da daliban ke irin wannan ziyara dajin Yankari.
” A duk shekara sai dalibai sun yi irin wannan tafiya domin yana daga ciki darussan sannan akan kasa su zuwa rukuni-rukuni. Rukunin farko da na biyu duk sun tafi sun dawo lafiya. Wadannan sune rukuni na uku da suka tafi. Sai dai bayan sun dawo ne aka fara samun bayanin wasu basu da lafiya.
” Yanzu dai an killace duk wadanda suka tafi Yankari din ana duba su. 12 kuma da suka nuna alaman tsanannin rashin Lafiya an garzaya dasu babban asibiti a Maiduguri.
Har yanzu dai ba a tabbatar da ko a can Yankari din bane daliban suka kamu da wannan cuta da ba asan ko wacce iri bace.
Sai dai kuma akwai rahoton cewa an samu irin wannan matsala bayan wasu dalibai a jihar Kano sun yi irin wannan ziyaya dajin Yankari din.
Discussion about this post