Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta damke wani mai suna Innocent Ifunayachi mai shekaru 34 da laifin yi wa ‘yar shekara 14 fyade.
Ifunayachi ya lallabi wannan yarinya ce a cikin gidan su a lokacin da ya ziyarci gidan ranar Laraba.
Kakakin rundunar jihar Legas, Bala Elkana ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai a jihar Legas.
Elkana yace Ifunayachi ya iske wannan yarinya ita kadai a falo zaune tana cin abinci. Da ya shigo sai ta mike tsaye domin kawo masa ruwan sha.
“Tashin wannan yarinya ke da wuya sai Ifunayachi ya barbadamata ganyen wiwi a cikin abincinta ya kuma gauraya abincin domin kada ta gane.
“Bayan ta mika masa ruwan ya sha sai ta koma ta ci gaba da cin abincin ta. Kafin ma ta gama cin abincin ta bingire barci ya kwashe ta.
Bayan haka rundunar ta kuma sake damke wasu matasa guda biyu masu suna Kazeem Bello mai shekaru 26 da Dayo Maker mai shekaru 24 da suka yi wa ‘yar shekara 13 fyade a watan Nuwanba 2018.
Elkana ya ce a dalilin tafka wannan ta’asa da wadannan matasa suka yi har ciki ya shiga sannan ma har ta haihu ‘ya mace.
“Yarinyar ta bayyana wa iyayenta cewa Bello da Maker sun yi mata barazanar kashe ta idan har ta gaya wa wani abin da suka yi mata.
Yace ‘yan sanda sun damke Maker, Bello ne dai har yanzo jami’ai na farautar sa.