A Dalilin yadda PREMIUM TIMES ta fallasa yadda tsohon Cif Jojin Najeriya, Alfa Belgore cewa shi ne ya taimaki kamfanin P&ID har ya shigar da Najeriya kara a kotun Birtaniya, aka ci tarar Najeriya naira tiriliyan 3.2, ’yan Najeriya sun nemi a kama shi kuma a hukunta shi.
Belgore wanda shi ne shugaban Kotun Kolin Najeriya tsakanin 2006 zuwa 2008, shi ne ya yi wa tsarin shari’ar Najeriya filla-filla, ya nuna wa kamfanin P&ID inda shari’ar Najeriya ke da nakasu, sannan kuma ya nuna musu yadda za su yi nasara a kan Najeriya idan kamfanin ya kai Najeriya kara kotu.
Kotun dai ta maka wa Najeriya hukuncin biyan P&ID diyyar naira tiriliyan 3.2 ta hanyar yin nazarin Dokar Karya Sharuddan Yarjejeniya ta 1996 ya Ingila da Wales da kuma Dokar Karya Sharuddan Yarjejeniya ta Najeriya ta 2004. Wato Arbitration Act, 1996 (England and Wales) da kuma Nigerian Arbitration and Conciliation Act, 2004.
Kudin da aka yanke wa Najeriya biyan diyya dai ya kai kashi 20 bisa 100 na dukiyar Najeriya da ke kasashen waje. Kuma idan har hukuncin ya tabbata, to daga cikin dukiyar ce za a zabtare kudaden diyyar. Hakan kuma idan har ya tabbata, to Ministar Harkokin Kudaden Najeriya, Zainab Ahmed ta ce ba zai yi wa dukkan ’yan Najeriya dadi ba, domin kowa sai ya ji a jikin sa.
LAUYOYI: Lauyoyi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa Alfa Belgore ya karya dokar kundin tsarin mulkin Najeriya da har ya kewaya ta bayan fage ya yi wa kamfanin P&ID aikin yadda zai kayar da Najeriya a kotu. Don haka ya kamata a kama shi a hukunta shi.
‘YAN NAJERIYA: ‘Yan Najeriya da dama sun harzuka ganin yadda ashe Alfa Belgore ne ya tadiye kafar Najeriya a kotu, har aka ci kasar tarar Naira tiriliyan 3.2. Don haka da dama sun fara kiraye-kirayen a hukunta shi kawai.
Karanta nan: Salsalar yadda aka janyo wa Najeriya asarar Naira tiriliyan 3.2
Ga yadda aka rika ragargazar Alfa Belgore a shafukan Twitter da Facebook, bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa shi:
BELGORE DAN ZAGON KASA: “Mohammed Abdulkadir ya bayyana cewa abin da Belgore ya yi cin amanar kasa ce, kuma zagon kasa ne. Ya kamata Majalisar Tarayya ta bijoro da wata dokar da za ta yi maganin irin wadannan mutane a cikin Kundin Dokar Najeriya. Ga irin ta nan mun gani Femi Falana ya na kare El-Zakzaky, duk kuwa da cewa mabiyan sa na kashe jami’an tsaro. Ya kamata doka ta rika kare ‘yan kasa, ba wai ta rika cutar da su ba.”
IDAN A CHANA NE BELGORE YA TASHI DAGA AIKI: “Shafin Twitter na wani mai suna @lookingupright kuwa cewa ya yi abin da Belgore ya yi cin amanar kasa ne. Idan a Chana ne, shikenan za su tashe shi daga aiki. Amma tunda a nan Najeriya ne, da ya kira waya daya an kira na biyu, shikenan sai a kashe maganar a ce daga sama ne aka ce a bar zancen.”
MAI HALI BA YA BARIN HALIN SA: Emma Akpasubi ya shiga shafin sa na Facebook ya bayyana Belgore da cewa “wannan labari ya nuna ashe har yanzu Belgore bai daina halin sa na harkalla da barankyankyama ba. To ‘yan Najeriya dai da kuma doka na nan sun zuba ido su ga yadda za a karke.”
BELGORE MUGU NE: Patrish Ojeba cewa ya yi, “kai, wannan mutumin mugu ne. Bayan ya sace kudaden talakawa tsawon shekaru, kuma daga baya ya kewaya ya sake talauta talakawa saboda tsananin rashin tausayi. Shin idan har wannan biyan diyya ta shafi aljihu na da na ku, to ya mu ka iya da ran mu?”
DAMA BA MU YI DACEN SA A KOTUN KOLI BA: Muhammed Bello cewa ya yi Belgore na daya daga cikin mutane marasa kishin kasar nan da aka yi rashin dacen shigar su harkar alkalanci, har ya kai matsayin shugabancin Kotun Koli.”
Mutane da dama irin su Aliyu Dauda, Niyi Karunwi, Jay Waref, Ojay Lawrence da Buchi Nwozulo duk sun ragargaji Belgore.
WAIWAYE:
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo cikakken wannan labari na yadda aka aka sa hannunn wannan yarjejeniyar harkallar wannan kawngila, a karkashin Ministan Harkokin Man Fetur na lokacin, Marigayi Rilwanu Lukman a lokacin da tsohon shugaba Umaru Musa ‘Yar’Adua ke kwance asibitin Saudiyya ya na jiyya.
Sannan kuma mun bada labarin yadda gwamnatin Goodluck Jonathan da ta Shugaba Muhammadu Buhari suka yi sakacin kin cika sharuddan sasantawa da kamfanin P&ID. Wannan jinkirin ne ya sa kamfanin fusata har ya garzaya kotu.
Discussion about this post