KIN JININ BAKI: Afrika Ta Kudu ta turo jakadun bai wa Najeriya hakuri

0

Shugaban Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya aiko tawagar jakadu uku zuwa Najeriya domin neman sasanci da bada hakuri bisa hare-haren da ‘yan kasar sa suka rika kai wa ‘yan Najeriya, sun a kashe su.

Jakadan zai kara jaddada wa Najeriya bukatar kada dankon hadin kai tsakanin kasashen Afrika, tare da tattauna hanyoyin da za a sake tabbatar da zaman lumana a tsakanin kasashen biyu.

An ruwaito cewa Kakakin Shugaba Ramaphosa mai suna Khusela Diko a ranar Lahadi ya na cewa “jakadun uku za su fara kai ziyara Najeriya sannan su karasa wasu kasashen Afrika shida.”

Ya ci gaba da cewa za su isar da sakon Shugaba Ramaphosa dangane hare-haren da aka kai wa ‘yan wadannan kasashe da ke zaune a Afrika ta Kudu da kuma lalata musu dukiyoyi da aka yi.

Sannan kuma za su kara jaddada matsayar Afrika Ta Kudu wajen bin doka da oda.

Dangantaka tsakanin Afrika Ta Kudu da Najeriya dai ta yi tsami biyo bayan hare-hare da kisan da aka rika yi wa ‘yan Najeriya a can kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da jakada na musamman domin bayyana wa Afrika ta Kudu rashin jin dadin Najeriya da irin wulakancin da aka rika yi wa ‘yan Najeriya a Afrika ta Kudu.

Wannan kashe-kashe ya janyo wa Afrika ta Kudu jangwangwama, domin kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito yadda aka rika yi wa Ramaphosa eho da sowa ana muzanta shi a wurin bikin bizne gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe.

Sannan kuma kasashen Botswana, Zambiya da Madagaska duk sun janye daga wasan kwallon kafa na sada zumunta da a da aka shirya yi tsakanin su da Kungiyar Bafana Bafana, ta Afrika ta Kudu.

Cikin makon da ya gabata ne Najeriya ta kwaso mutane 178 daga Afrika ta Kudu. Sannan kuma ana sa ran dawowar wasu 320 a yau Litinin.

Share.

game da Author