Gwamnati za ta tallafa wa mutane 9,000 da jalin sana’ar kiwin kifi a Kebbi

0

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya bayyana cewa gwamnati zata tallafa wa mutane 9,000 da kudade da kayan aiki domin fara sana’ar kiwon kifi a jihar Kebbi.

Osinbajo ya fadi haka ne a taron kaddamar da shirin tallafa wa mutane domin fara sana’o’in hannu na shirin ‘Trademoni’ da aka yi Birnin Kebbi ranar Alhamis.

Ya ce burin gwamnati shine ta kafa cibiyoyi na sana’o’in hannu a kalla guda daya a kowani jiha a kasar nan.

Tun a 2017 ne gwamnati ta kaddamar da wannan shiri, zuwa yanzu kuwa an tallafa wa mutane 400,000 a fadin kasarnan.

“Jihar Kebbi ce jiha na 24 da zai ci moriyar wannan shiri. Wanda mutane 9000 zasu samu tallafin.

A karshe Osinbajo yayi kira ga hukumomi da masana’antu da su rika tallafawa da mara wa shirin gwamnati baya domin samun nasara akai.

Share.

game da Author