Hukumar kula da ilimin firamare na jihar Kaduna (SUBEB) ta kammala shiri tsaf domin saka yara 145,000 wanda basu da ilimin boko a makarantun firamare a jihar.
Mataimakin shugaban hukumar Ibrahim Aminu ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kaduna ranar Laraba.
Aminu yace hukumar ta horas da ma’aikata 2,000 da za su wayar da kan iyayen da ‘ya’yan su basu da irin wannan ilimin mahimmancin saka ‘ya’yan su a makarantun firamare.
Ya ce wannan shiri na saka yara a makarantun firamare na karkashin shirin samar da ilimin firamare na babbar bankin duniya (BESDA) sannan burinsu shine saka yaran da basu da ilimin boko 727,764 a makarantun firamare nan da shekaru 10.
“A lissafe dai idan duk kauye a jihar Kaduna ta saka akalla yara 35 da basu da ilimin boko a makarantun firamare a cikin lokaci kalillan za mu cimma burin mu.
“A yanzu haka ma’aikata 2000 din da muka horas sun fara aiki sannan har mun kuma saka yara sama da 100 a makarantun firamare dake jihar.
A karshe jami’in hukumar SUBEB Habib Alhassan ya bayyana cewa hukumar ta fara horas da malaman firamare 6,828 domin koyar da dalibai darusan boko da harshen Hausa.
“Burin mu shine mu saka yara 727,764 wanda basu da ilimin boko a makarantun firamare sannan mun wadatar da malamai da kayan aiki domin samun nasarar haka.