’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban da Sakataren Kungiyar Malaman Manyan Kwalejin Fasaha ta Oyo da ke Igbo-Ora.
An sace Opadijo Olujide tare da wasu mutane hudu, kamar yadda Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bayyana.
Malamin ya na koyarwa ne a College of Agriculture and Technology ta jihar Oyo.
PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa Olujide da shi Sakataren Kungiyar, Gbenga Alayande da wasu mutane uku duk an sace su a kan hanyar su ta dawowa daga wani taron da suka halarta a garin Saki, a ranar Alhamis.
“Al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis. Su na kan hanyar dawowa ne daga taro, aka yi garkuwa da su, su biyar. Hudu daga cikin su malaman kwalejin ne. Daya kuma matar daya daga cikin su ce.
Haka wani ya shaida wa manema labarai, amma ya ce kada a bayyana sunan sa.
“Amma hukumar kwalejin na ta kokarin ganin an sako su. Su kuma ‘yan sanda na biye da al’amarin.
Shi kuma Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Jihar, Olugbenga Fadeyi, wanda ya tabbatar da yin garkuwa da malaman, ya ce jami’an su na ci gaba da binciken al’amarin.
“Shi ma Kwamishinan ’Yan Sanda da kan sa ya je inda lamarin ya faru, domin ganin wurin da idon sa.” Inji kakakin.