Sarkin Anka, Maimartaba Attahiru Ahmed ya gargadi maza da su gujewa yin aure barkatete da tare Iyalan da baza su iya kula da su ba.
Sarki Ya kara da cewa za ka ma’aikacin gwamnatin da albashin sa bai wuce naira 15,000 a wata ba ya tara mata a gidansa sannan suyi ta haihuwa bayan ya ba zai iya kula da su.
” Hakan shine ke kara yawan talauci a kasarnan. Dole dai sai mutum na da halin iya rike iyalansa sannan zai kara idan ba haka ba kara saka kai cikin matsanancin talauci ne kawai na babu gaira babu dalili.”
Yace idan mutum ya ajiye iyalai daidai karfinsa, zaka ga sun taso cikin kula sannan za su samu ilimi da tarbiyya mi nagarta.
Sarki yayi wannan gargadi ne a wajen rabon kayan masarufi da wargidan gwamnan jihar Zamfara, Aisha Bello-Matawalle ta yi a karamar Hukumar Anka da wasu kananan hukumomin jihar.