Kasashen Afrikan da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ke tallafa wa sun jajirce cewa za su dauki tsauraran matakai domin dakile yaduwar cututtuka a kasashen su.
A taron da aka gudanar a Brazzaville kasar Congo ranar Laraba kasashen tare da hadin guiwar WHO sun kaddamar da wata takarda dake dauke da wadannan tsauraran matakai da suka ga zai fi dacewa wajen dakile yaduwar cututtuka.
Matakan da aka tsara zai dauki kasashen tsawon shekaru 10 kafin a iya aiwatra da su. Sannan hakan zai taimaka wajen hana yaduwar cututtuka kamar su Ebola, zazzabin lassa da sauran su.
Bincike ya nuna cewa bullowar cututtuka irin haka ya zama ruwan dare a kasashen Afrika inda kasashen basu yin kwanaki hudu ba tare da wani cuta ya bullo ba. Hakan kuma nada nasaba ne da canjin yanayi,yaduwar cututtuka daga wasu wuraren a dalilin tafiye-tafiyen mutane, da dai sauran su.
Shugaban tarayyar kasashen Afrika dake samun tallafi daga WHO Matshidiso Moeti ya bayyana cewa wadannan matakan dakile yaduwar cututtuka za su fi tasiri ne idan gwamnatocin kasashen Afrika sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin haka ya tabbata.
Moeti yace hakan ya hada da yi wa hukumomin hana yaduwar cututtuka tanajin isassun kudaden da za su bukata, daukan kwararrun ma’aikatan da za su rika yin bincike da sa ido wajen saurin gano bulluwar cuta cikin gaggawa da sannan samar da magungunan da ya kamata domin kawar da cutar da wurin gaske.
A karshe taron ya yi kira ga WHO da sauran kungiyoyin bada tallafi da tsu rika taimakawa wa wadannan kasashe domin samun nasara da burin cimma abinda aka sa a gaba.