Matsalolin da ake fama da su a fannin kiwon lafiyar kasarnan – Sambo

0

Shugaban Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta kasa (NHIS) Mohammed Sambo ya bayyana cewa Najeriya za ta iya samun nasara burin samar da kiwon lafiya ta gari a farashi mai sauki wa kowa da kowa idan ta tilasta wa mutanen shiga tsarin inshoran kiwon lafiya.

Sambo ya fadi haka ne a taron inganta aiyukkan hukumar da aka yi a jihar Kaduna ranar Laraba.

Ya ce tilasta wa mutane shiga tsarin shirin hanya ce da za a rika samar da isassun kudaden domin iya bunkasa shirin ga wadanda basu ciki.

Sambo yace za a samu nasarar haka ne idan aka gyara dokar da ta kafa hukumar Inshorar Kiwon Lafiya.

Tuni dai har majalisar dattawa ta mika wa shugaba Muhammadu Buhari gyaran dokara kafa hukumar da tayi domin maida ita doka. Sai dai kuma har yanzu shugaba Buhari bai saka hannu a kai ba.

Daga nan sai Sambo yace hukumar ta sake komawa ga majalisar dattawa domin a sake duba dokar ta yadda shugaba Buhari zai gaggauta saka hannu a kai ta zama doka.

Inshorar Kiwon Lafiya

Tun da gwamnati ta kafa shirin inshoran kiwon lafiya a kasar nan a 2005 shirin bata taka rawan gani ba wajen inganta kiwon lafiyar mutanen Najeriya.

Babban dalilin kafa shirin kuwa shine domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen Najeriya cikin sauki amma hakan bai samu ba duk da miliyoyin kudaden da aka rika jida wa hukumar domin ta yi aiki tun bayan kafa ta.

Wasu ‘Yan Najeriya suna yi korafin cewa adadin yawan mutane dake cikin tsarin basu wuci kashi biyar zuwa 10 bisa 100 ba. Kuma wadanda suke cikin wannan tsari basu basu samun kula yadda yakamata.

Matakan da za abi don inganta Shirin

Sambo ya ce mataki na farko da zai fi maida hankali akai don samun ci gaba a hukumar shine a fara gyara dokar da ta kafa hukumar. Daga nan kuma sauran abubuwan sai su biyo baya.

Share.

game da Author