FIFA ta ki amincewa a buga Gasar Kofin Duniya na Mata a Kaduna

0

Alamomi na nuni da cewa da wahala Kaduna ta karbi bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya na Mata ‘yan kasa da shekara 20 da za a gudanar a Najeriya, domin Hukumar Shirya Gasannin Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta na tababar amincewa da buga wasa a filin wasan Kaduna.

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya main tushe cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya na matukar son a zabi wata jihar daga Arewa ta kasnce daya daga cikinn masu karbar bakuncin wasan, musamman Kaduna.

Sai dai kuma FIFA ta ki amincewa da wannan bukata ko shawara da NFA ta kawo, saboda dalili na tsaro.

Wasu jami’an da ke cikin tattaunawar sun gulmata wa PREMIUM TIMES cewa Shugaban NFA, Amaju Pinnick na ta kokarin ganin an amince da Kaduna domin ta wakilci Arewa a matsayin birnin da za a buga wasu wasannin a Arewa din.

Cikin shekarun 1999 da 2009 dai Kaduna, Kano da Bauchi duk sun karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya ta matasa.

Amma kuma a yanzu FIFA ta na tababa sosai saboda matsalar rashin tsaro a yankin Arewa. Dalili kenan ta ki amincewa da Kaduna a cikin biranen da za a buga gasar a cikin shekara ta 2020.

Baya ga fargabar Boko Haram da ta ke yi, FIFA na tsoron irin jerin gwanon zanga-zangar neman a saki shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da mabiyan sa ke yi.

Ranar Litinin ne wakilai biyar daga FIFA za su dira Lagos domin fara duba filayen wasan da za a gudanar da gasar, da kuma irin kayan da kowane filin wasa ya tanada.

Za su shafe kwanaki hudu sun a wannan duba-gari. Daga Lagos za su danna Benin, sai Asaba sai kuma Uyo.

Kasashe 16 ne za su fafata a wannan kasaitacciyar gasa, wadda ita ce za ta kasance ta goma tun bayan kirkiro gasar da aka yi.

“FIFA ta ce wa Najeriya idan har ta tubure ta ce sai an kai wasu wasannin a Kaduna, to FIFA za ta nemi wata kasar ta shirya daukar nauyin gasar, ba Najeriya ba.

Pannick ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba zai yi magana ba galle har ya ce komai a wannan blamari.

Share.

game da Author