Hukumar Kula da Saida Man Fetur ta Kasa, wato DPR, shiyyar Kaduna, ta kulle gidajen saida man fetur da gas har 56 a cikin jihar Kaduna.
DPR ta bayyana cewa ta kulle gidajen man ne saboda sun ki bin ka’idojin da suka jibinci sayar da fetur a gas a fadin duniyar nan.
Babban Jami’in DPR mai kula da Shiyyar Kaduna, Isa Tafida ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zagayen gani-da-ido a kan gidajen mai na watan Yuli a jihar Kaduna.
Ya ce sun gudanar da samamen kulle gidajen mai din ne domin zakulo masu boye mai da masu karkatar da shi da kuma masu saidawa sama da adadin da aka kayyade farashin kowace lita.
“ Mun kulle wasu gidajen saida mai ne saboda su na karkatar da mai, ba su sayar da shi gaba daya a gidan mai. Wasu kuma su na harkokin mai a gidajen mai din da ba su da lasisi, ko kuma wadanda lasisin su ya kare, amma sun ki zuwa a sabunta musu.
“ Sauran kuwa mun kama su ne su na saida mai a wuraren da babu matakan tsaron lafiya a gidajen mai din, ko kuma rashin cika sharuddan bin dokokin kare hadurra ko rashin kula da muhimmancin rayuwar jama’a da dukiyoyin su.” Inji Tafida.
Ya kara da cewa sun ziyarci gidajen mai 354 a fadin Jihar Kaduna inda suka samu ana saida lita daya kasa da Naira 143 zuwa 145 ka’idar da aka yanke wa lita daya.
Tafida ya kasa da cewa an ziyarci gidajen saida gas har guda 19.
“ An kulle gidajen mai 53, 11 daga cikin su saboda kin sayar da mai ana karkatar da shi, 40 saboda kin bin ka’idar dokar saida man fetur da rashin kiyaye ka’idar lafiya da rayuka da kiyaye dukiyoyi da sauran su.”
Ya gargadi masu saida mai su guji jefa kan su da gidajen man su cikin hada-hadar hakalla.
Discussion about this post