HAJJI 2019: Hukumar Aikin Hajji ta kammala kwashe maniyyatan Najeriya

0

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta kammala kwashe dukkan maniyyata aikin Hajjin bana daga Najeriya zuwa Saudiyya.

An kammala kwashe maniyyatan ne a jiya Laraba, kamar yadda Kakakin Yada Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara ta bayyana.

Ta yi jawabin ne a lokacin da jirgin karshe mai dauke da jami’an NAHCON ya tashi daga filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a jiya talata.

Usara ta kara da jewa jiragen sama sun yi jigilar kai maniyyata har sau 93, inda aka kwashi mutane 44,450.

“Jirgin karshe ya bar Abuja a yau da safe, dauke da mutane 301 daga jihohin kasar nan daban daban.

“Jami’an NAHCON sun tashi zuwa Saudiyya, bayan sun tabbatar da cewa ba a bar maniyyaci ko daya a Najeriya da zai yi korafin cewa an tafi an bar shi ba.

NAHCON sun gode wa kamfanonin jiragen saman da suka yi zirga-zirgar kwasar maniyyata.

Ta kuma gode wa Hukumar Jin Dadin Alhazai ta kowace jihar kasar nan. Ta kuma yi fatan za su nunka karincin da suka yi idan an fara kwaso Mahajjata zuwa Najeriya, bayan kammala aikin Hajji.

Idan ba a manta ba, NAHCON ta sanar da rasuwar ‘yan Najeriya biiyar, wadanda a cikin su akwai mata uku da maza biyu.

Sannan kuma ta yi gargadi tare da bayar da shawarar yadda mahajjatan Najeriya za su kula wajen kauce wa kamuwa da cututtuka.

Share.

game da Author