Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya Kori duka sakatarorin Kananan Hukumomi 14 dake Jihar kuma har ya nada sabbi.
Darektan Yada Labaran Gwamna Matawalle, Yusuf Idris, ya bayyana cewa an umarci tsoffin sakatarorin su mika takardun barin aiki ga ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu.
Wadanda aka nada sun hada da Abubakar Bakura, Bakura, Rabiu Pamo, Anka; Abdulkadir Gora, Birnin-Magaji; Lawali Zugu, Bukkuyum; Sani Mainasara, Bungudu, Rabiu Hussaini, Gummi, Nura Musa, Gusau, Bashir Bello, Kaura-Namoda, Ahmadu Mani, Maradun, Salisu Yakubu, Maru, Abba Atiku, Shinkafi; Ibrahim Garba, Talata-Mafara; Aliyu Lawali, Tsafe da Bala Dauran na karamar hukumar Zurmi.
Bayan haka gwamna Matawalle ya nada Sha’ayau Marafa, sabon shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Ta Audu gusau dake Talatan mafara.
Haka kuma gwamnan ya tabbatar da nadin Muhammad Maradun a matsayin Rajistaran wannan Kwaleji.