Kashi 20 bisa 100 na ‘yan Najeriya na fama da matsalar tabuwar hankali – likita

0

Wani likitan da ya kware a fannin duba masu fama da tabuwar hankali a jihar Zamfara Aremu Sa’ad ya bayyana cewa kashi 20 bisa 100 na ‘yan Najeriya na fama da tabuwar hankali.

Aremu ya kuma ce da dama daga cikin wannan kason na fama da wannan matsala ba tare da sun sani ba.

Ya fadi haka ne da yake hira da manema labarai a garin Gusau.

Aremun yace ya gano hake ne bayan mahawara da tattance sakamakon binciken da kwararrun likitoci suka gudanar a shekarun da suka gabata game da ‘gejin’ hankalin mutane a kasar nan.

” Bayan mahawara da tattance sakamakon bincken da na yi na gano cewa akalla kashi 20 bisa 100 na mutanen kasar nan na fama da tabuwar hankali. Sannan na kuma gano cewa masu fama da wannan matsala za su iya warkewa idan kwararren likita ya dubasu su kuma marasa lafiyan suka daure wajen kiyaye sharuddun shan magani yadda ya kamata.

Aremu yace idan ba haka ba masu fama da wannan matsala za su ci gaba da zama cikin wannan hali.

Ya ce akan gaji tabuwar hankali ko kuma mutumin da ke ta’ammali da miyagun kwayoyi da ababen dake sa maye ko kuma idan mutum ya fada cikin damuwa.

A karshe Aremu yace gwamnati za ta iya shawo kan wannan matsala ne idan ta kirkiro shirye-shirye da kafa dokokin da za su taimaka wajen gina asibitocin da masu fama da tabuwar hankali za su rika samun kula sannan da wayar wa mutane kai game da illar nuna wa masu fama da wannan matsala kiyayya.

Share.

game da Author