Cutar Hepatitis B ya fi cutar Kanjamau illa a jiki- Likita

0

Bello Kumo likita ne dake aiki da asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Shika Zaria, ya bayyana cewa cutar Hepatitis B ya fi cutar kanjamau yi wa jikin mutum lahani fiye da yadda ake tunani.

Kumo ya fadi haka ne a taron wayar da kan mutane kan cutar Hapatitis B wanda Gidauniyar ‘Kashim Ibrahim Fellows (KIF) ta shirya a garin Kaduna.

Ya ce wayar da kan mutane kan wannan cuta zai taimaka wajen samar musu da kariya daga kamuwa da cutar sannan da dakile yaduwar ta.

” Da dama dake dauke da wannan cuta basu da masaniyar cewa suna dauke da shi sannan basu da masaniyar cewa wanda ke tsaye kusa da su ka iya kamuwa da cutar balle har su iya neman magani domin su ceci kan su ba.

” A dalilin haka mutane da dama ke mutuwa sannan yaduwar cutar ta ki ci ta ki cinyewa.

Kumo yace za a iya kamuwa da Hepatitis B idan mai dauke da cutar ya yi tari ko kuma atishawa,idan zufa ko jinin mai dauke da cutar ya shafi wanda baya dauke da cutar isan yana da budadden ciwo.

Ya ce hanyar samun kariya daga kamuwa da cutar shine idan mutane na yin gwajin cutar akai-akai da kuma yin rigakafi.

” Da zaran kayi gwajin cutar kuma sakamakon ya nuna cewa baka dauke da ita kamata yayi mutum ya yi rigakafin cutar amma idan mutum na dauke da cutar sai ya gaggauta fara shan magani domin hana yaduwar cutar.

Bayan haka da yake mika godiyarsa ga Gidauniyar KIF kan shirya wannan taro gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya ce samun nasaran dakile yaduwar cutar ya dogara ne ga irin goyan bayan da mutane za su bada.

Ya ce kamata ya yi mutane su zo a hada hannu da gwamnati domin ganin an samu nasarar dakile yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba a 2018 ne El-Rufa’I ya kafa gidauniyar ‘Kashim Ibrahim Fellows domin inganta rayuwar matasa a jihar yadda za su zama shugabanni na gari nan gaba.

A wannan shekar kungiyar KIF ta kebe mako daya daga ranar Litini zuwa juma’a domin ingata rayuwar mutane a jihar.

Bayan haka kuma gidauniyar zata horas da matasa sana’o’in hannu kamar gyaran kai na mata, aski da wayar wa mutane kai game da mahimmancin tsaftace jikinsu da muhallinsu.

Share.

game da Author